Kun san cewa Abdul El-Sayed na iya zama Musulmi na farko da aka zaɓa a matsayin ɗan Majalisar Dattijan Amurka?
Yana takarar a jam’iyyar Democrat a jihar Michigan, kuma takararsa ta ja hankalin Shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya soki ra’ayoyinsa.
🎥 — Muhammad Buhari Fagge
Wannan rubutun da matashiya Boina ta yi game da dalilin da ya sa ta rufe ɗakin kwalliyarta ya tayar da hankalin sauran ƙananan masu kasuwanci.
Ƙarin bayani - bbc.in/48nglHv
A zaɓen majalisar dokokin Isra'ila, masu adawa da Firaminista Benjamin Netanyahu suna ƙoƙarin kawo ƙarshen shugabancin ɗan siyasar da ya kafa tarihin zama mafi daɗewa a kan mulki.
Ƙarin bayani - bbc.in/4zbr1oJ
Ɗan wasan gaba ɗan ƙasar Portugal, Gustavo Varela, yana cikin wadanda Arsenal ke sa ido a kai; Crystal Palace na son ci gaba da riƙe dan wasan gefe Ismaila Sarr.
Ƙarin bayani - bbc.in/4ij8UpE
Yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan nasarar da haɗakar siyasa tsakanin Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso za ta iya samarwa a arewacin ƙasar, tambayar da ake yi ita ce ko hakan kaɗai zai haifar masa da nasara a faɗin Najeriya.
Ƙarin bayani - bbc.in/4zdTZEo
Kyaftin din Ingila, Harry Kane ya ci ƙwallo 73 a dukkanin wasannin da ya buga wa kungiya da tawagar ƙasa a kakar wasan 2025-26.
Ko da yake an umarci masu kada ƙuri’a su yi la’akari da kakar wasa ta baya-bayan nan kawai lokacin tsara jerin ‘yan wasa.
Kwallo 156 da Kane ya ci a wasa 158 da ya buga wa Bayern Munich tun daga shekarar 2023 sun ɗaga shi zuwa matsayi na bakwai a jerin fitattun masu cin ƙwallaye a tarihin kungiyar Jamus.
Baturen ƴansanda reshen Dutsinma da ke jihar Katsina, CSP Auwalu Gwadabe ya tabbatar wa BBC cewa wasu da ba a san su wane ba ne suka je gidan malamin, inda suka harbe shi.
Bayanai sun ce lamarin ya faru ne yayin da Sheikh Masussuka ke shirin karatu da yammacin ranar Litinin.
Bayan isowar ʼyanwasan da wasu fitattun mutane ne aka fara bikin inda za a karrama ɗanwasa mafi ƙwazo a duniya a birnin Landan.
Ga yadda wasu suka isa wurin taron yayin da suka caɓa ado.
Tace hoto - Abdulrazzaq Kumo
Wata ƙungiyar ɗalibai masu zanga-zangar neman sauyi ce ta lashe babban zaɓen ƙasar Serbia, inda ta doke tsohon shugaban ƙasar Aleksandar Vucic, wanda ya shafe shekaru 14 yana mulki.
A nata ɓangaren, ƙungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'ah Wa'iƙamatus-Sunnah (JIBWIS), wadda ake danganta matasan da ita, ta ce ta ɗauki mataki kan lamarin.
Ƙarin bayani - bbc.in/3U2ROEp
Waɗanda aka tantance sun haɗa da Ibrahim Namadi Dala da Mukhtari Ishaq Yakasai da kuma Farfesa Sani Lawan Malumfashi. Sauran sun haɗa da Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa da Idris Garba Mustapha, sai kuma Salisu Yushaʼu Soja.
Ƙarin bayani - bbc.in/4zmjROc
Ana ci gaba da tafka muhawara kan wanda da ya cancanci lashe kyautar Ballon dʼOr ta ɗan wasa mafi ƙwazo a duniya a bana, kafin bikin da za a gudanar da yammacin yau.
Wa kuke ganin zai lashe wannan kyauta?
🎥 - Raabiʼatu Kabir Runka
Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka, FBI, ta ce za ta ci gaba da yaƙi da ƙungiyoyin damfara na ƙasa da ƙasa da ke sace wa Amurkawa biliyoyin daloli.
Ƙarin bayani - bbc.in/4sJoC2d
A yau Litinin ne za a karrama ɗan wasan ƙwallon ƙafa mafi ƙwazo a duniya da kyautar Ballon dʼOr a birnin Landan da ke Ingila.
Ana sa ran ɗaya daga cikin waɗannan manyan ʼyan takara uku ne zai lashe kyautar.
Kalli yadda girgizar ƙasa mai maki bakwai ta faru a Tibet.
Girgizar ƙasar ta yi sanadin mutuwar mutum 16, kuma hukumomi sun ayyana dokar ta ɓaci a yankin.
Kwamitin, wanda ya ƙunshi manyan ƴan siyasa da tsofaffin masu riƙe da muƙaman gwamnati, zai kasance cibiyar tsara dabaru da daidaita ayyukan yaƙin neman zaɓen Peter Obi da Kwankwaso
Ƙarin bayani: bbc.in/3TWBnJN
Masu hasashe sun sanya ƴan wasan gefe na Sifaniya, Lamine Yamal, da kyaftin ɗin Ingila, Harry Kane, da ɗan wasan gaban Real Madrid a matsayin waɗanda ke kan gaba a takarar lashe babbar kyautar.
Karin bayani - bbc.in/47Z9Afb
Ministan lafiyar Najeriya ya tabbatar da cewa an fice da matar da ke ɗauke da cutar Ebola daga Najeriya zuwa Switzerland tare da mijinta inda za ta ci gaba da samun kulawa.
Ya kuma ce tana samun sauƙi sannan sun gano wasu mutum 53 da ake tunanin matar ta yi muʼamala da su.
Ƴanbindiga sun kai hari ƙauyen Binnari da ke ƙaramar hukumar Karim Lamido, jim kaɗan bayan sallar Juma'a, inda suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi, tare da ƙona shaguna da babura.
Ƙarin bayani - bbc.in/4ke427B















