Tech Hausa (@TechHausa) header
Tech Hausa (@TechHausa) profile picture

Kafar watsa labarai kimiya da fasaha cikin harshen Hausa. || Tech media platform that shares technology news and stories in Hausa Language.

Nigeria
Joined September 2019
Photo by Tech Hausa (@TechHausa)Photo by Tech Hausa (@TechHausa)Photo by Tech Hausa (@TechHausa)Photo by Tech Hausa (@TechHausa)Photo by Tech Hausa (@TechHausa)Photo by Tech Hausa (@TechHausa)Photo by Tech Hausa (@TechHausa)Photo by Tech Hausa (@TechHausa)Photo by Tech Hausa (@TechHausa)Photo by Tech Hausa (@TechHausa)
Bankin fasahar kuɗi na OPay ya buɗe sabon ofishinsa a jihar Kano, a wani mataki na faɗaɗa ayyukansa da kuma ƙara kusantar da hidimomin kuɗi ga abokan cinikinsa a Arewacin Najeriya. An gudanar da bikin buɗe ofishin a ranar Laraba 4 ga Nuwamba, 2026, tare da yanka cake, inda aka buɗe ofishin da ke kan titin Hadejia Road, kusa da kasuwar Yankaba, a gefen bankin Keystone Bank. Kamfanin ya bayyana cewa buɗe sabon ofishin wani ɓangare ne na ƙoƙarinsa na samar da sauƙaƙaɗɗun hidimomin kuɗi masu inganci da kuma kusantar da su ga mutane da 'yan kasuwa a yankin. A halin yanzu, sabon ofishin ya fara aiki, inda kwastomomi za su iya zuwa domin samun taimako, yin tambayoyi da kuma warware matsalolin da suka shafi ayyukan bankin na OPay. Wannan mataki na ƙara faɗaɗa kasancewar OPay a Arewacin Najeriya, tare da samar wa masu amfani da shi damar samun taimakon kamfanin kai tsaye ba tare da dogaro da manhaja ko hanyoyin intanet kaɗai ba. Bayan jihar Kano, wacce jiha ce kuke ganin ya kamata Bankin na Opay ya sake buɗe ofishin nasa saboda Kwastomomin sa?
1
1
55
Wani direban kamfanin inDrive ya rasa motarsa a hannun wasu ’yan fashi da makami a yankin Ajao Estate da ke jihar Lagos, bayan mutanen sun yi amfani da manhajar kamfanin wajen yin hayar motar a matsayin fasinjoji. Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:30 na asuba a ranar 25 ga Oktoba, inda maharan suka yi amfani da bindiga wajen yi wa direban barazana, suka tilasta masa fita daga motar sannan suka tsere da ita. Bayan faruwar lamarin, kamfanin inDrive ya tabbatar da cewa ya dakatar da asusun fasinjan da ake zargi da hannu a lamarin, yayin da yake gudanar da bincike na cikin gida. Kamfanin ya kuma bayyana shirinsa na haɗa kai da rundunar ’yan sanda domin gudanar da bincike, tare da ɗaukar matakan da suka dace bayan kammala binciken. Sai dai matakin da kamfanin ya ɗauka ya sake tayar da muhawara kan ingancin hanyoyin tantance fasinjoji da kuma matakan kare direbobin da ke amfani da manhajojin sufuri. Ƙungiyar direbobin sufuri ta manhajojin intanet a Najeriya, wato Amalgamated Union of App-based Transporters of Nigeria (AUATON), ta nuna damuwarta kan yadda kamfanonin ke tabbatar da ainihin mutanen da ke yin rajista da amfani da manhajojinsu. Ƙungiyar ta kuma jaddada buƙatar samar da tsarin taimakon gaggawa da zai iya kare direbobi idan suka shiga irin wannan haɗari. A zahiri, dakatar da asusun fasinja bayan faruwar laifi ba zai iya mayar da motar da aka sace ba, ko kuma kawar da haɗarin da direban ya fuskanta. Abin da ya fi muhimmanci shi ne samar da matakan kariya tun kafin fara tafiya, kamar ingantaccen tantance fasinjoji, tabbatar da lambar waya da bayanan mutum, hanyar aika saƙon gaggawa ga jami’an tsaro, da kuma tsarin bin diddigin tafiya idan aka samu matsala. Wannan lamari ya sake buɗe muhawara kan nauyin da ya rataya a wuyan kamfanonin sufuri na intanet wajen kare direbobinsu, musamman waɗanda ke aiki da daddare ko a wuraren da tsaro ke da rauni. Shin kamfanonin irin su inDrive, Uber da Bolt suna buƙatar ƙarin matakan tsaro kafin su amince da kowace tafiya? Wane irin tsari ya kamata a samar domin kare rayuka da dukiyoyin direbobi?
47
Today at the GTA 2.0 — Kano 2026 💚
2
2
44
Birnin Kano ya shiga sabon babi na tarihi a fannin fasaha da tattalin arziki, yayin da aka buɗe taron Global Tech Africa (GTA 2026) a Amani Events Center a wannan rana ta hau Taron, wanda aka gudanar a karon farko a yankin Sahel da Arewacin Nijeriya, ya haɗa daruruwan masana fasaha, ’yan kasuwa, masu zuba jari da jami’an gwamnati domin tattauna yadda fasahar zamani za ta iya zama babbar hanyar bunƙasa tattalin arzikin yankin. A wannan karon, ba batun amfani da fasaha kawai ake yi ba. Babban abin da ake nema shi ne yadda za a koma daga amfani da fasaha zuwa ƙirƙira, sarrafa kayayyaki da gina masana’antun zamani. GTA 2026, wanda FutureMap Foundation ta shirya tare da haɗin gwiwar NITDA, MTN Nigeria da Qorebox Solutions, yana gudana ne ƙarƙashin taken: "Connecting Africa, Accelerating Growth: Industrialization, Market Access & the Sahel Gateway." Me Ya Sa Aka Zaɓi Kano? Kano ba kawai birni ne mai yawan jama'a ba. Ita ce ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin kasuwanci da ke haɗa Arewacin Nijeriya da sauran ƙasashen yankin Sahel. Rahotanni sun nuna cewa Kano na taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da kasuwancin kan iyaka, wanda aka kiyasta darajarsa tsakanin dala biliyan 2 zuwa biliyan 5 a kowace shekara. Tare da faɗaɗa kasuwancin Afirka ta hanyar AfCFTA, wannan damar na iya ƙaruwa sosai. Masana sun bayyana cewa lokaci ya yi da Arewa za ta daina dogaro da saye da amfani da kayayyakin fasaha kawai, ta koma samar da nata kayayyaki, ƙirƙira da sarrafa su ta amfani da fasahar zamani. A bayyane yake cewa GTA 2026 na ƙoƙarin sake fasalta matsayin Kano a taswirar tattalin arzikin Afirka. Amma babban ƙalubalen ba wai kawai jawo masana fasaha da masu zuba jari zuwa Kano ba ne, shi ne samar da yanayin da zai ba 'yan Arewa damar ƙirƙira, sarrafa kayayyaki da gina kamfanonin fasaha masu gogayya a kasuwannin duniya. Idan aka cimma wannan buri, Kano ba za ta kasance kawai wurin da ake sayar da kayayyakin fasaha ba, za ta iya zama wurin da ake ƙirƙira da samar da su. Amma banda masana'antu da fasaha, wace sabuwar dama ce GTA 2026 zai budewa matasan Arewa, 'yan kasuwa da masu zuba jari?
69
Wata ƙungiyar masu aikata laifukan intanet (Hackers) mai suna BYOD ta nemi afuwar marasa lafiya bayan ikirarin kai wani harin yanar gizo kan cibiyar lafiya ta Jami'ar New Mexico Health Sciences Center da ke Amurka. Ƙungiyar ta kuma yi alkawarin biyan duk wani mara lafiya da harin ya shafa kuɗin diyya har dala $2,500, idan har zai iya gabatar da shaidar yadda harin ya shafe shi. Lamarin ya faru ne a ranar 26 ga Oktoba, 2026, inda harin ya haddasa tsaiko a ayyukan asibitin, ciki har da karkatar da motocin ɗaukar marasa lafiya zuwa wasu asibitoci tare da dakatar da wasu tiyata da alƙawuran ganin likitoci. A cikin saƙon da ƙungiyar ta wallafa a shafinta, ta ce ba ta san cewa wasu daga cikin na'urorin kwamfutocin da ta kulle suna gudanar da ayyukan da ke taimaka wa likitoci wajen kula da marasa lafiya a zahiri ba. Saboda haka, ta ce za ta bayar da maɓallan buɗe na'urorin da aka kulle (Decryption Keys) kyauta ga ɓangaren asibitin kawai. Ƙungiyar ta bayyana cewa: "Muna da ɗabi'a da zuciya, mu ba miyagu ba ne." Sai dai, duk da neman afuwar, ƙungiyar ta ce za ta ci gaba da riƙe bayanan da ta yi ikirarin sacewa daga cibiyar, lamarin da ke nuna cewa har yanzu akwai barazanar fallasa bayanan sirrin marasa lafiya da ma'aikata. A nata ɓangaren, jami'an jami'ar sun tabbatar da cewa an samu matsalar tsaro ta yanar gizo, amma sun ce binciken farko ya nuna cewa wasu na'urorin ma'aikata ne suka samu matsala, ba manyan kwamfutoci da sabar (Core Servers) na cibiyar ba. Jami'ar ta kuma yi gargaɗin cewa marasa lafiya kada su amince da duk wani saƙon da ke neman bayanan sirri ko na kuɗinsu bisa sunan biyan diyya, saboda masu aikata laifin na iya amfani da lamarin wajen yi musu zamba. A halin yanzu, ba a tabbatar da cewa ƙungiyar ta biya wani mara lafiya diyya ko kuma ta miƙa maɓallan buɗe na'urorin ba.
108
Wani lauya ya maka kamfanin sadarwa na MTN a kotu, yana neman diyyar ₦10 miliyan bisa zargin cewa kamfanin ya riƙa cire wa mahaifiyarsa kuɗin kati ta hanyar shigar da ita wasu hidimomin da ake biya ba tare da cikakken izininta ba. A cewar lauyan, mahaifiyarsa tsohuwa ce da ba ta iya karatu ko fahimtar saƙonnin da ke bayyana a wayarta. Ya ce duk lokacin da irin waɗannan saƙonni suka bayyana, takan danna maɓallin “OK” ne kawai domin su ɓace daga allon wayarta. Sai dai, lauyan ya yi zargin cewa danna wannan maɓalli ya sa aka riƙa shigar da mahaifiyarsa wasu hidimomin da ake cire kuɗin kati a kai a kai, duk da cewa ba ta fahimci abin da take amincewa da shi ba. Ya zargi MTN da cin gajiyar rashin iya karatunta, lamarin da ya jawo mata asarar kuɗi. Wannan ba shi ne karon farko da MTN ke fuskantar irin wannan ƙorafi ba. A watan Disambar 2024, Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta umarci kamfanin ya biya wani abokin cinikinsa, Ezugwu Anene, diyyar ₦15 miliyan kan saƙonnin da bai nema ba da kuma cire masa kuɗin kati kan hidimomin da ya ce bai yi rajista da su ba. Lamarin ya sake tayar da muhawara kan ko danna maɓallin “OK” yana nufin mutum ya fahimci abin da yake amincewa da shi. Musamman ga tsofaffi da mutanen da ba su iya karatu, ya kamata a samu hanyoyin tabbatar da cewa sun fahimci hidimar da za a riƙa cire musu kuɗi a kanta. Sai dai, zargin da ake yi wa MTN a wannan sabon shari'ar yana jiran tantancewar kotu.
33
Kamfanin OpenAI ya faɗaɗa tsarin tallan ChatGPT Ads zuwa Najeriya da Afirka ta Kudu, inda 'yan kasuwa za su iya tallata hajojinsu ga masu amfani da ChatGPT yayin da suke neman shawarwari kan kayayyaki ko ayyukan da suke buƙata. A cewar bayanan farashin da aka bayyana, mafi ƙarancin kuɗin talla shi ne dala $25 a rana. Idan aka gudanar da tallan na tsawon kwanaki 30, kuɗin zai kai dala $750, wanda zai iya haura naira miliyan 1, gwargwadon canjin kuɗi da sauran caji. 'Yan kasuwa za su iya amfani da tsarin OpenAI Ads Manager wajen tsara tallansu, zaɓar kasuwar da suke son kaiwa da kuma saita kasafin kuɗinsu da tsawon lokacin tallan. OpenAI ta bayyana cewa za a ware tallace-tallacen da alamar talla domin kada a rikita su da amsoshin ChatGPT. Kamfanin ya kuma ce masu talla ba za su samu damar ganin sirrin tattaunawar masu amfani ba, kuma tallace-tallacen ba za su rinjayi amsoshin AI ba. Wannan sabon tsarin na iya samar wa 'yan kasuwar Najeriya wata hanya ta isa ga abokan ciniki yayin da suke tunanin abin da za su saya. Sai dai tambayar ita ce: Shin za ka iya kashe kusan naira miliyan 1 a wata domin tallata kasuwancinka a ChatGPT, ko kuwa za ka fi son Instagram da Google Ads?
46
Kamfanin Vatar, wanda ya ƙirƙiri wasan intanet na Lagos Life, na tattaunawa da masu zuba jari domin samun sabon jari na dala miliyan 2.5, bayan wasan ya samu masu amfani sama da miliyan 10. A farkon ƙaddamar da wasan, kamfanin ya samu jarin dala 500,000, wanda ya kai darajarsa dala miliyan 10. Daga cikin masu zuba jarin akwai wanda ya kafa Flutterwave, Olugbenga Agboola, da O.O. Nwoye da Abdulhamid Hassan na Mono, da Nathan Nwachukwu na Terra Industries. Sabon jarin na iya ɗaga darajar kamfanin zuwa tsakanin dala miliyan 15 da dala miliyan 30. Lagos Life wasa ne da ke ba mutane damar ƙirƙirar hoton kansu na zamani, samun ayyukan yi, hulɗa da wasu, sayayya da mallakar gidaje ko filaye a birnin intanet. Wasan ya fara ne da birnin Ikoyi na Legas, inda ya samu rajistar masu amfani miliyan 1 cikin kwanaki 3 kacal. Kamfanin na shirin faɗaɗa shi zuwa Abuja da Fatakwal. Ya kuma fara samun kuɗaɗen shiga ta tallace-tallace da tallata waƙoƙin mawaka, inda kuɗin shigarsa suka haura dala 170,000. Shalom Rayhamen, wadda ta kafa kamfanin, ta ƙirƙiri wasan cikin dare guda ta hanyar amfani da fasahar zamani. Nasarar Lagos Life na nuna yadda 'yan ƙirƙira a Afirka za su iya amfani da fasahar AI wajen gina wasanni da sabbin hanyoyin kasuwanci a intanet.
72
Yarjejeniyar da Hukumar Kare Bayanai ta Ƙasa (NDPC) ta yi da kamfanin Meta ta jawo tambayoyi kan yadda ake tabbatar da bin dokokin kare bayanan sirri a Nijeriya, musamman bayan rahoton tara kamfanin $32.8 miliyan kan zargin karya dokokin bayanai. A watan Oktoba 2025, Meta da hukumar sun cimma yarjejeniya, wadda kotu ta amince da ita a watan Nuwamba. Yarjejeniyar ta soke tarar, yayin da Meta ta ci gaba da kasancewa ƙarƙashin wasu wajibai na bin dokokin ƙasar, ba tare da amincewa da aikata laifi ba. A shekarar 2026, Meta ta ƙara shiga shirye-shiryen haɗin gwiwa da hukumomin gwamnati, ciki har da ƙaddamar da GovGuide Nigeria da shirin wayar da kai kan kare bayanai tare da NDPC. Wannan ya sake tayar da tambayar yadda haɗin gwiwar gwamnati da kamfanonin fasaha zai shafi aikin sa ido da tabbatar da doka. A gefe guda, kamfanonin fasahar kuɗi na cikin gida suna fuskantar wa'adin Babban Bankin Nijeriya na Janairu 2027 kan adana da sarrafa bayanan mu'amalar biyan kuɗi a cikin ƙasar. Bin waɗannan ƙa'idoji na iya buƙatar ƙarin kuɗi da sauye-sauye a tsarin fasaharsu. Muhimmin batu shi ne tabbatar da cewa ana amfani da ƙa'idojin kare bayanai cikin adalci ga duk kamfanoni, na cikin gida da na ƙasashen waje. 'Yan Nijeriya ma suna buƙatar ƙarin bayani kan abin da yarjejeniyar Meta ta ƙunsa da matakan da ake ɗauka don kare bayanan sirrinsu.
149
Kamfanin Meta ya bayyana cewa sama da mutane miliyan 10 a Amurka da Kanada sun riga sun kafa nasu mataimakin basirar wucin gadi na Muse AI cikin watanni 1.5 kacal da fara amfani da shi. Shugaban kamfanin, Mark Zuckerberg, ya bayyana hakan yayin gabatar da rahoton kuɗin shiga na Meta, inda ya ce Muse na samun karɓuwa cikin sauri, har ya kai matsayin manhajar da ta fi kowace manhaja a App Store a kusan kowace rana. Ya kuma ce kusan kashi 25% na mutanen da suka kafa Muse suna amfani da shi a kowace rana. Zuckerberg ya ce mafi yawan masu amfani da Muse suna amfani da shi ne wajen siyayya ta intanet, inda sama da kashi ɗaya bisa huɗu na masu amfani da manhajar ke yin hakan. Ya ƙara da cewa matsakaicin kuɗin sayen kaya ta hanyar manhajar ya haura dala $200. Meta na shirin mayar da Muse wani mataimaki na zamani da zai taimaka wa mutane gudanar da ayyukansu, amfani da imel da kalanda, siyayya, adana lokaci da kuɗi, har ma da gina kasuwanci. Kamfanin ya ce zai samar da manhajar kyauta ga mafi yawan masu amfani, sannan ya samu kuɗin shiga ta hanyar cajin wasu kasuwanci kan cinikayyar da Muse ya taimaka wajen gudanarwa. Haka kuma, masu buƙatar ƙarin fasaloli za su iya biyan kuɗin rajista. Zuckerberg ya ce Meta na sa ran inganta ƙarfin sarrafa bayanan Muse domin rage kuɗin gudanar da shi da fiye da ninki 10 cikin shekara guda, yayin da kamfanin ke shirin faɗaɗa amfani da fasahar ga biliyoyin mutane a nan gaba.
1
60
Bayan shafe shekaru 5 yana jagorantar @AltSchoolAfrica, @AdewaleYusuf_ ya sauka daga matsayin shugaban gudanarwar kamfanin, inda zai ci gaba da kasancewa mamba a kwamitin gudanarwa. Abokin kafa kamfanin, @hackSultan , ne zai maye gurbinsa. Yusuf ya bayyana cewa matakin ya samo asali ne daga buƙatar samun ƙarin lokaci da nutsuwa wajen kula da rayuwarsa da iyalansa, bayan shafe shekaru yana tafiye-tafiye tsakanin Amurka da Afirka. A ƙarƙashin jagorancinsa, AltSchool Africa ta bunƙasa daga cibiyar koyar da fasahar zamani zuwa babbar makarantar horas da ƙwararru, inda ta horar da ɗalibai sama da 100,000 daga ƙasashe 75 na duniya. Sabon shugaban, Akintunde, na shirin faɗaɗa ayyukan makarantar ta hanyar ba ɗalibai damar samun takardar shaidar Diploma, sannan su ci gaba da karatun digiri a jami'o'in da ke haɗin gwiwa da AltSchool. Manufar ita ce sauƙaƙa samun ilimin jami'a mai inganci a farashi mai rahusa. Wannan sauyi na iya buɗe sabon babi ga AltSchool Africa, daga koyar da sana'o'in fasaha zuwa samar da hanyoyin samun shaidar digiri ga ɗaliban Afirka. Amma lokaci ne zai nuna yadda sabon tsarin zai sauƙaƙa musu samun ilimin jami'a.
41
In less than 24 hours, a single post on our Facebook page reached 1.2 million people Millions of Hausa speakers remain an untapped audience for many brands. Want to reach new customers in a language they understand? @TechHausa is your bridge to that audience. Let's collaborate
2
3
90
Wani sabon rahoton kamfanin PaidHR ya fitar ya nuna cewa ma’aikata 46 cikin 100 a Najeriya suna samun albashin da bai kai ₦200,000 a wata ba. Binciken ya ƙunshi ma’aikata sama da 25,000 daga kamfanoni da ma’aikatu sama da 400, bisa bayanan da aka tattara har zuwa Yuli 2026. Rahoton ya nuna cewa ma’aikaci na tsakiya a Najeriya yana samun ₦217,000 kafin cire haraji da kuɗin fansho, yayin da kusan ma’aikata 10 cikin 100 ke samun ƙasa da ₦70,000 a wata. Haka kuma, ma’aikata 10 cikin 100 ne kawai ke samun albashin ₦1m ko sama da haka a kowane wata. Binciken ya kuma bayyana cewa albashi ya bambanta sosai bisa fannin aiki. Ma’aikatan fasaha da AI suna samun matsakaicin albashin ₦418,916, yayin da na kasuwanci da baƙuncin baƙi ke samun kusan ₦80,000. A bangaren jinsi kuma, mata suna samun matsakaicin albashin ₦192,789, idan aka kwatanta da ₦238,103 na maza. Rahoton ya gano cewa karin albashi yakan fi yawa a shekarun farko na fara aiki, amma bayan shekaru 5, samun karin albashi mai tsoka yana ƙara wahala. Wannan na iya sa ma’aikacin da ya daɗe a kamfani ya riƙa samun ƙasa da sabon ma’aikaci da aka ɗauka bisa sabon farashin kasuwa. Duk da hasashen cewa matsakaicin albashi na iya kaiwa ₦380,000 nan da 2030 idan ana samun karin albashi na 15% a kowace shekara, rahoton ya yi gargaɗin cewa hauhawar farashin abinci, sufuri da gidaje na iya rage ƙarfin sayen ma’aikata. Wannan na nuna cewa samun albashi mai yawa ba lallai ya nufin ingantuwar rayuwa ba ne idan kuɗin ba sa iya biyan buƙatun yau da kullum.
1
95
Ta ɓoye ta fito fili, gabanin shirye-shiryen OPay na sayar da hannun jari a Amurka (IPO), inda bayanan kuɗaɗe suka nuna cewa kamfanin ya tafka mummunar asara ta sama da Naira biliyan 150 ($118.36 miliyan) saboda taurin kan masu cin bashi a Najeriya. Manhajojin ba da bashi na kamfanin kamar su EaseMoni sun fada tarkon ’yan Najeriya bayan sun rarraba jimillar bashi na dalar Amurka miliyan $927.6 (kimanin ₦tiriliyan 1.28), sai dai kuma kwatankwacin dala $1.28 a cikin kowace dala $10 da aka bayar rance ta kafe, lamarin da ya tilasta wa OPay lashe amansa ta hanyar goge kuɗaɗen a matsayin asarar bashi (Expected Credit Loss). Ko da yake kamfanin yana ƙoƙarin rufe fuskarsa da cewa ya sami dalar Amurka miliyan $236.12 ta hanyar tsauraran ruwa da tsinallen tara (interest and penalties), wannan gagarumar badakalar rashin biyan bashi ta girgiza harkar ba da lamuni ta intanet a ƙasar. Shin kana Daga cikin masu cin bashin Opay? Ka biya naka ko kaima ka cikin wadanda suka riƙe masu kuɗi?
1
62
Sterling Bank da cibiyar tallafawa sana’o’i ta Cascador sun haɗa gwiwa domin ƙaddamar da wani babban asusun tallafin bashi na dalar Amurka miliyan 200 domin taimakawa ƙananan sana’o’i da matsakaita a Najeriya wajen samun lakadan bashin gudanar da sana’o’insu. Wannan sabon shiri yana da nufin raba kasadar bashi tsakanin asusun da cibiyoyin ba da bashi, wanda hakan zai bawa bankuna kwarin gwiwar fitar da babban bashi na dogon lokaci. Cascador ta bayyana cewa wannan tsari yana da damar fadada ikon bayar da bashi har zuwa dalar Amurka biliyan guda a tsawon lokaci. Gidajen sana’o’in da wannan shiri ya sa gaba sune waɗanda suka riga suka nuna ƙarfin tafiyar da bashi amma suke fuskantar ƙalubalen samun nasara wajen ciro kuɗaɗen daga bankuna. A matakin farko, kasuwancin da suka dace za su iya samun bashin kuɗin gida da ya yi daidai da dalar Amurka dubu 250, tare da burin buɗe ƙofar samun bashin da ya kai dalar Amurka miliyan guda da zarar asusun ya cika gaba ɗaya. Shugabar gudanarwa ta Cascador, Trish Thomas, ta bayyana cewa ta hanyar raba kasada tsakanin masu ba da bashi da kuma amfani da amincin al’umma a matsayin wata shaida mai ƙarfi ga bankuna, asusun zai taimaki kasuwanni da dama wajen samun abin da suke buƙata domin faɗada kasuwancinsu da kuma samar da abun yi ga mutane. Ana saɓon gina tushen kuɗaɗen wannan asusu ne daga agajin ƙungiyoyin sa-kai, masu zuba jari domin rage radadin al’umma, da kuma cibiyoyin kuɗi na ci gaba. Wannan mataki ya biyo bayan fitar da wata takardar nazari ta Cascador mai taken The Multiplier Model, wacce ta nuna cewa kashi 22 kacal na sana’o’i a yankin kudu da hamadar Sahara ne ke da asusun bashi na banki, wanda ya yi ƙasa sosai da matsakaicin adadin duniya na kashi 36. Obinna Ukachukwu, wanda yake gudanarwa a bankin Sterling Bank, ya bayyana cewa wannan tsari zai haɗa kasuwancin da aka ba da shawararsu daga cibiyoyin zuba jari da ke da cikakken saninsu. A cewarsa, wannan tsari zai kawo masu cin bashi ingantattu gami da sauƙaƙe duba ƙarfin kasuwancinsu da ci gaba da sa ido a kansu, wanda ke ba banki kwarin gwiwar ba su babban bashi na lokaci mai tsawo. Za a tafiyar da wannan asusu ne ta hanyar kamfanin Riverwell Platform Holding Limited wanda yake mallakar ƙasar Birtaniya gami da reshensa na Riverwell Platform Services Nigeria. Shi kansa asusun ajiyar za a riƙe shi a keɓe, kuma Obinna Ukachukwu zai kasance ɗaya daga cikin daraktocin dandalin na Riverwell. Wannan sabon tsari ya ginu ne a kan gwajin da Cascador da Sterling Bank suka yi a baya. Cascador ta bayyana cewa tun daga shekara ta 2019 ta samun nasarar tallafawa kasuwanni 80 wanda hakan ya taimaka musu wajen tara kuɗaɗen zuba jari da suka wuce dalar Amurka miliyan 150.
49
Kamfanin Apple ya kaddamar da wata sabuwar na'ura mai kwakwalwa ta gida mai suna 'Apple HomeView' akan farashin $299 (₦403,650). Wannan na'ura, wadda take da babban dan ƙaramin allo mai girman inci 7, tana amfani da sabon tsarin fasahar zamani na Siri AI da kuma gajeren sassa na A18 chip domin tafiyar da al'amuran gida cikin sauki. Za a fara sayar da ita a hukumance ranar 13 ga watan Nuwamba, 2026. Abubuwan da na'urar ta kunsa sun hada da: Na'urar na iya gane fuskokin mutane har su shida a gida guda, inda take canza abubuwan da ke kan allo domin nuna sako da jadawalin kowane mutum daban. Manhajar Siri da take iiya amfani da bayanan mai amfani da ita domin gudanar da ayyuka a cikin manhajoji daban-daban cikin sauri. Allon na'urar yana kulfe kansa kai tsaye idan wani bako ko wanda ba a sani ba yayi yunkurin leken asirin mai na'urar. Tana iya nuna hoton kyamarori tara na gida a lokaci guda, kuma tana aiki tare da sabbin kayayyakin gida na kamfanonin LG da Schneider Electric.
1
2
140
Wata babbar sanarwa mai firgitarwa ta gidauniyar fasaha a kasar Kenya da ma shiyyar Afirka baki daya ta fito fili bayan da kamfanin Microsoft ya sanar da ma'aikatansa cewa yana shirin rufe cibiyarsa ta Africa Development Centre wato ADC da ke birnin Nairobi a ƙasar Kenya Wannan mataki da aka bayyana wa ma'aikatan a ranar Litinin 12 ga watan Oktoba na shekarar 2026 yana zuwa ne a matsayin wani bangare na sauye-sauyen da kamfanin ke yi a matakin kasa da kasa domin sake tsara fasalin gudanar da ayyukansa. Cikin daftarin labarin da ake samu daga cikin ma'aikatan sun nuna cewa al'amarin ya girgiza bangaren fasaha na kasar Kenya sosai domin cibiyar ta kasance daya daga cikin manyan ginshiƙan bunkasa hazakar matasa a fannin da sarrafa na'ura mai kwakwalwa da tsara aikace-aikace. Duk da cewa kamfanin Microsoft bai fito fili ya bayyana adadin ma'aikatan da wannan rufe bangaren zai shafa ba a halin yanzu cibiyar da ke gini mai suna Dunhill Towers a yankin Westlands na birnin Nairobi tana dauke da tsakanin kwararrun ma'aikatan fasaha 450 zuwa 570. Kamfanin ya fayyace cewa wadannan sauye-sauye da ake shirin yi sun shafi sashen injiniyanci kawai yayin da sauran ayyukansa na kasuwanci da kuma tallata hajoji gami da ba abokan ciniki goyon baya za su ci gaba da gudana a kasar Kenya ba tare da wata tsaiko ba. Sakamakon wannan labari sakataren ma'aikatar watsa labarai da fasahar sadarwa ta kasar Kenya William Kabogo ya gudanar da wani taro na gaggawa da manyan shugabannin kamfanin Microsoft domin tattaunawa kan hanyoyin kiyaye basira da gwaninta ta ma'aikatan cikin gida na kasar Kenya gami da kare ayyukan su. Bangarorin biyu a halin yanzu suna gudanar da aiki tare domin fito da wani tsari guda wanda zai maida hankali sosai kan bunkasa amfani da fasahar basira ta AI da mayar da ayyuka tsarin na'ura mai kwakwalwa da kuma karfafa tsaro a yanar gizo.
1
235